Alamu na nuna cewa, nan da dan lokaci, dakarun sojin Najeriya za su kwato garin Gwoza dake jihar Borno daga hannun mayakan Boko Haram.
Hakan, a cewar wakilin al'ummar mazabar Borno sanata Mohammed Ndume, ya biyo bayan kwazon da sojojin ke nunawa a baya bayan nan.
Sanata Ndume ya ce, cikin makwanni 5 da suka gabata, sojojin kasar sun kwato garuruwa 22 daga ikon mayakan kungiyar.
Garin Gwoza wanda ke da nisan kilomita 135 arewa da birnin Maiduguri, fadar gwamnatin jihar Borno, ya kasance helkwatar mayakan Boko Haram tun cikin shekarar da ta shude.
Rahotanni daga Najeriyar na nuna cewa, sojojin kasar na ci gaba da fatattakar mayakan Boko Haram daga garuruwa, da yankunan da suka kwata a baya, ciki hadda Bama dake jihar ta Borno a arewa maso gabashin kasar.
Sojojin Najeriyar na samun tallafi daga dakarun kasashen Nijar, da na Kamaru da Chadi, kasashen dake makwaftaka da Najeriyar, wadanda kuma su ma suka taba dandana hare-haren mayakan na Boko Haram. (Saminu)