Kasar Togo ta yanke shawarar aiwatar da babban zabenta a ranar 15 ga watan Afrilun mai zuwa, kamar yadda wata sanarwa da aka fitar ta nuna.
A cikin sanarwar an ce, dukkan 'yan takara za su biya kudin kasar sefa miliyan 20 kwatankwacin dalar Amurka 34,593 domin sayen takardar nuna bukatar shiga takarar, kuma gaba daya kudin da za'a kashe wa al'umma wajen yakin neman zaben zai kai sefa miliyan 600.
Sharuda da sakamakon dake shafi hakan wadanda ba'a riga an bayyana ba suna karkashin dokokin kasar, in ji sanarwar.
Faure Gnassingbe, shugaban kasar mai ci yanzu shi ma ana sa ran zai sake tsayawa takara a karo na uku. Ya dai karbi ragamar mulkin kasar ne a shekarar 2005, aka sake zabe shi a shekarar 2010. (Fatimah)