Mataimakin sakatare janar na MDD kan harkokin siyasa, Jeffrey Feltman, ya bayyana damuwarsa a yayin da yake ziyarar aiki a birnin Lome a ranar Talata kan tsarin demokaradiyya, sahihanci da gaskiya game da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisu da za su gudana a farkon watanni uku na shekarar 2015 a kasar Togo, in ji jaridar Togo-Presse ta kasar.
Muna fatan wadannan zabuka za su amsa bukatun al'ummar kasar Togo, kuma za su gudana cikin gaskiya ba tare da magudi ba, in ji mista Jeffrey Feltman bayan ganawa tare da shugaban kasar Faure Gnassingbe, a cewar jaridar Togo-Presse.
Mista Feltman ya tattauna kan batutuwan zaman lafiya da tsaro a shiyyar yammacin Afrika tare da shugaba Faure Gnassinbge, da ma kuma taimakon da kasar Togo ta nema wajen tsare tsaren zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisu a farkon watanni uku na shekarar 2015.
Kasar Togo ta nemi taimakon MDD domin wadannan zabuka, kuma wannan na da muhimmanci gare ni wajen sauraren shugaban kasar Togo da yin nazari kan dangantakarmu a wannan fanni, in ji mista Jeffrey Feltman.
MDD na daga cikin sahihan abokan huldar kasar Togo, inda take ci gaba da kawo taimakonta ga wannan kasa a wajen shirya zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisu.
Tuni dai tsarin ci gaba na MDD UNDP ya samar da tallafi wajen horar da jami'an tsaro 8000 domin zabukan shekarar 2015.
Haka kuma a cikin watan Janairun da ya gabata, UNDP ya rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyin tallafin kudi na Sefa miliyan 205 tare da babbar hukumar dake kula da watsa labarai da sadarwa ta kasa (HAAC) da kuma wasu kungiyoyin fararen hula goma. (Maman Ada)