Tawagar hadin gwiwar MDD da kungiyar AU a kasar Sudan UNAMID, ta bayyana rashin jin dadin ta, don gane da ruruwar rikici a yankin Dafur, dake kudancin kasar Sudan.
Cikin wata sanarwa da tawagar ta fitar, ta ce, fadace-fadacen baya bayan nan da suka auku, tsakanin wani sashe na dakarun gwamnatin kasar da mayakan 'yan tawaye, sun janyo asara mai tarin yawa.
Rahotanni sun bayyana cewa, tashin hankalin baya bayan nan da ya auku a yankin Um Gunya, mai tazarar kilomita 50 daga kudu maso gabashin Nyala, ya janyo kone kauyuka da dama, tare da sanya al'ummun yankin kauracewa gidajen su. Da yawa daga irin wadannan mutane na samun mafaka a sansanin 'yan gudun hijira na Al Salam da Kalma.
UNAMID ta zargi gwamnatin kasar Sudan da kin amincewa ta shiga wuraren da rikicin ya fi kamari, duk kuwa da burin da ake da shi na baiwa fararen hular dake sassan kariya.
Kawo yanzu dai rundunar sojin kasar ba ta ce komai ba, don gane da rahotannin da tawagar ta fitar, game da halin da ake ciki. (Saminu)