in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan Boko Haram sun hallaka mutane 75 lokacin da suka kwace garin Gwoza
2015-03-26 09:58:14 cri

Mazauna garin Gwoza na jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, sun ce, mayakan Boko Haram sun yi wa a kalla mutane 75 yankan rago, lokacin da suka kwace garin watanni 6 da suka gabata.

Wasu da suka tsira da rayukansu lokacin farmakin na garin Gwoza, sun shaida wa kamfanin dillancin rabarun kasar Sin Xinhua cewa, 'yan Boko Haram din sun kuma yi awon gaba da mata da dama yayin wannan balahira.

Wata mata mai suna Mairo Mohammad, wadda ta samu kubuta yayin harin, ta ce, mayakan sun rarraba mutanen garin wuri wuri, sa'an nan suka rika yanka wasu kamar dabbobi.

Ta ce, baya ga wadanda suka hallaka, mayakan sun kuma yi awon gaba da wasu maza su kimanin 25, wadanda kawo yanzu ba a ji duriyarsu ba. Mairo ta ce, ita da wadanda suka samu damar tserewa, sun yi tafiyar kusan kilomita 70 zuwa birnin Yola, inda suka samu tallafi daga wani jami'in gwamnati mazaunin garin.

Mayakan Boko Haram dai sun kwace garin Gwoza dake kan iyakar Najeriya da Kamaru ne tun cikin watan Satumbar bara, bayan sun tarwatsa al'ummomin yankunan dake makwaftaka da garin, suka kuma kafa abin da suka kira daular musulunci a garin.

A makon da ya gabata ne dai dakarun sojin Najeriyar suka ayyana garin na Gwoza, cikin yankunan da ba a kai ga kwatowa daga hannun mayakan na Boko Haram ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China