in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Namibia ta yi gyara a kundin tsarin mulkin kasar
2014-08-29 10:33:15 cri

Majalisar dokokin kasar Namibia ta amince da wata dokar gyara a kan kundin tsarin mulki na kasar a karo na ukku, duk da kasancewar 'yan adawar na kasar da kungiyoyin kare hakkin bil'adama, suna nuna fargabar cewar, gyaran fuskar kundin tsarin mulki zai bai wa shugaban kasar ta Namibia karin karfin iko.

Dokar da ta amince da gyaran tsarin mulkin, wacce aka gabatar da ita ga majalisar dokokin kasar, ta ba da damar kafa ofishin mataimakin shugaban kasar, tare da kara yawan kujeru a majalisar wakilai ta tarayyar kasar daga 72 zuwa 96, haka zalika canjin ya sa a yanzu majalisar dattawa ta kasar na da kujeru 42, a maimakon 26 da ake da su a da.

Sauran canje-canjen da suka biyo gayran kundin tsaarin mulkin sun hada da kara adadin mutanen da shugaban kasa zai baiwa mukami daga majalisar dokokin kasar daga gurabe 6 zuwa 8, da kuma kafa hukumar leken asiri ta Namibia, wacce shugaban kasa ne zai zabi shugabanta.

A halin da ake ciki, jam'iyyu 'yan adawa na kasar suna ikirarin cewar, ba'a tuntube su ba kafin majaliar dokokin kasar ta yi saurin amincewa da gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulki na kasar. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China