Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya yi kiran da a kawo karshen tashe tashen hankali da nuna kyamar baki dake ci gaba da bazuwa a wasu jahohin kasar da dama.
Wadannan tashe tashen hankali sun shafi birnin Johannesburg, inda aka wawashe wasu shaganun dake hannun 'yan kasashen waje a yayin hartabo tsakanin baki da 'yan kasar a ranar Laraba, lamarin da ya jikkata mutane da dama.
Rikicin da ya barke a Johannesburg ya biyo bayan irin wadannan tashe tashen hankali da suka faru a makwannin baya a wasu unguwanin dake kewayen birnin Durban.
Tashe tashen hankali sun yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar da jikkata wasu da dama. An kashe kayayyakin daruruwan shaguna dake hannun 'yan kasashen waje dake zaune a kasar, haka kuma an kaurar da miliyoyin baki daga yankunan da ke fama da rikici.
Ina ganin ya kamata a dakatar da wadannan tashe tashen hankali ba tare da bata lokaci ba, domin bai kamata ba mu ci gaba da kashe junanmu, in ji mista Zuma.
Rikicin baya bayan nan ya barke dalilin rashin jin dadin daruruwan 'yan Afrika ta Kudu dake zargin 'yan kasashen waje da shigowa cikin kasar ba bisa doka ba, da gudanar da harkokinsu ba bisa doka ba, suna hana 'yan kasar Afrika ta Kudu samun aikin yi, da kuma aikata laifuffukan kisa.
'Yan kasashen waje da wannan matsala ta fi shafa su ne wadanda suka fito daga kasashen Malawi, Somaliya, Habasha, Najeriya da na sauran kasashen Afrika.
Gwamnati tana sane da damuwa da bacin rai na 'yan kasar Afrika ta Kudu, kuma tana aiki tukuru domin bullo da hanyoyin da za su taimaka wajen tabbatar da zaman jituwa tsakanin baki da 'yan kasa, in ji shugaban kasar Afrika ta Kudu.
A cikin wata sanarwar kungiyar tarayyar Afrika (AU) da aka fiyar a ranar Laraba, shugaban kwamitin tarayyar Afrika (AU) Nkosazana Dlamini Zuma ta bayyana cewa, ba za'a rufe ido ba kan wadannan hare hare kan 'yan kasashen waje da ke yankin KwaZulu-Natal na kasar Afrika ta Kudu, ita kuma yi kira da a kawo karshen wannan rikici ba tare da bata lokaci ba, tare da nuna damuwarta kan dalilan da ke janyo kyamar baki. (Maman Ada)