Rundunar sojin kasar Sudan ta Kudu, ta ce, dakarunta sun hallaka mayakan sa kai bangaren 'yan adawar kasar su 28, yayin wani dauki ba dadi da ya auku tsakanin sassan biyu a jihar Upper Nile.
Da yake tabbatar da aukuwar hakan, kakakin rundunar sojin kasar Philip Aguer, ya ce, fada ya barke tsakanin bangarorin biyu ne bayan da dakaru masu biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar, suka kai hari a yankin Jilshal dake kusa da kogin Sobat, yankin dake tsakanin birnin Al-Nasir da garin Malakal.
Philip Aguer ya kara da cewa, sojojin kasar sun hallaka dakarun 'yan adawar ne, a kokarin hana su mamaye yankin, inda suka amshe makamai da albarusai masu yawa daga gare su. Ya kuma ce, sojojin na ci gaba da farautar ragowar wadanda suka tsere cikin dazuzzukan yankin. (Saminu)