in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Pakistan a koda yaushe zasu tsaya tare, su tafe tare inji Shugaba Xi
2015-04-21 20:31:25 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping yace kasar sa da Pakistan zasu tafi tare a koda yaushe kuma al'ummar Sinawa zasu tsaya tare da su.

Shugaba Xi ya fadi hakan ne lokacin da yake jawabi gaban majalissun dokokin biyu na kasar, yana mai bayyana Pakistan a matsayin abokiyar Sin da za'a iya dogaro da ita tare da jaddada cewa dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu sakamakon mutunta juna da goyon baya ne.

Shugaban na Sin ya isa Islamabad ne a ranar litinin a ziyarar sa ta farko kasashen waje a wannan shekarar a matsayin muhimman makwabtan juna kuma zai bar Islamabad a yau din nan ya isa kasar Indonesiya domin halartar taron kolin Asia da Afrika da kuma bukukuwan cika shekjaru 60 da taron Bandung.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China