in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta sake jan hankalin bangarorin Libya da su dakatar da kaiwa juna hari
2014-12-30 09:49:10 cri

Tawagar UNSMIL ta MDD dake kasar Libya ta yi tofin Ala-tsine, game da hare-haren da aka kaddamar a birnin Misrata, tana mai kira ga daukacin bangarorin kasar dake adawa da juna, da su gaggauta dakarar da bude wata.

A cewar kakakin tawagar, hare-haren irin wadanda ake gani a yanzu haka, ba za su warware matsalar da ake fuskanta ba, illa dai kawai sake rura wutar gaba, da kara tabarbarewar yanayin tsaron kasar.

Kaza lika mai magana da yawun tawagar ta UNSMIL ya tunatar da masu kaddamar da hare-haren cewa, suna haifar da babbar illa ga burin da ake da shi na warware rikicin kasar ta hanyar lumana, matakin da ya sabawa kudurin kwamitin tsaron MDD, na wanzar da zaman lafiya a kasar.

Wannan ne dai karon farko da sojojin kasar ta Libya, masu samun goyon bayan kasashen duniya suka kaddamar da hare-hare ta sama a birnin Misrata, birni na uku mafi girma a kasar ta Libya, wanda kuma ke matsayin sansanin dakarun da suka taba amshe birnin Tripoli, fadar gwamnatin kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China