in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dalibai da dama sun ci abincin da ya lalace a Afrika ta Kudu
2015-03-02 15:10:58 cri

Daruruwan daliban firamare ne a Afrika ta Kudu aka kwantar a asibiti sakamakon cin abincin da ya lalace, kamar yadda jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance DA ta sanar a ranar Lahadi, inda ta tabbatar da cewa, ta samu rahotannin kwantar da yaran a asibiti a Sekhukhune dake gundumar Limpopo a karshen makon da ya gabata sakamakon abincin da aka ba su a makarantar suna shirin bayar da abinci ga dalibai wanda kuma ya riga ya lalace.

Wannan tabbacin ya fito daga sashin ilimi na gundumar Limpopo, in ji jam'iyyar ta DA.

Wannan lamari wanda shi ne karo na biyu da ya faru cikin watannin hudu wato yawan daliban da cin lalataccen abinci karkashin shirin bayar da abinci ya yi wa illa a gundumar Limpopo, in ji Jacques Smalle, shugaban jami'iyyar mai kula da dokoki, aikin gona, baitul malin, ka'idoji da da'a da kuma ilimi na wannan gunduma.

A watan Nuwamban bara ma daruruwan dalibai a Sekhukhune aka kwantar a asibiti sakamakon cin abincin da ya lalace.

Wannan ganganci da ake yi da rayuwan dalibai a Limpopo ba kawai ya tsaya a kan abincin lalatacce ba ne. A watan Satumbar bara, kusan dalibai 300 aka kwantar a asibiti bayan da aka samu gilashi a cikin abincinsu da wasu matsaloli kusan irin hakan a watan Oktoban dake biye. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China