in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Afrika ta Kudu na bukatar kara ganin masana'antu a hannun bakaken fata
2015-03-26 10:45:28 cri

Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ya yi alkawari a ranar Laraba na cimma burin gudanar da sauye sauyen tattalin arzki masu tattare da karin masana'antu da sauran hanyoyin sarrafawa a hannun 'yan Afrika bakar fata.

Muna fatan kara ganin masana'antu da sauran hanyoyin sarrafawa a hannun 'yan Afrika bakar fata domin mu samu damar cewa mun kai ga cimma burin sauya tattalin arziki, in ji mista Zuma a yayin da yake bude wani ginin Black Industrialist Indaba dake Midrand, dake arewacin birnin Johannesburg.

Bukatar ganin kamfanonin bakaken fata a cikin tattalin arziki ba ya da wata manufar kafa wani bambancin launin fata, sai dai ma kawar da wannan matsala, in ji Jacob Zuma, tare da bayyana cewa, jam'iyyar African National Congress wato ANC dake mulki, ta mai da wannan aiki a matsayin burinta na kawo sauyi mai zurfi ta fuskar zaman al'umma da tattalin arziki da zai kawo alheri da kasar Afrika ta Kudu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China