in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya nuna fushinsa game da hari kan tawagar majalisar a Mogadishu
2014-12-04 09:59:39 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya nuna fushinsa game da harin ta'addanci da aka kai a kan ayarin ma'aikatan majalissar a birnin Mogadishu na kasar Somaliya, kamar yadda wata sanarwa da kakakin sa ya fitar ke nunawa.

Wani 'dan kunar bakin wake ne dake tukin wata mota makare da ababen fashewa ya abka wa ayarin motocin ma'aikatan majalissar a babban birnin kasar Somaliya da sanyin safiyar Laraba, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 4.

A cikin sanarwa, Ban Ki-moon ya ce, babu wata hujja ta ta'addanci ko kai harin ta'addanci, kuma MDD ta kuduri aiki da al'umma da gwamnatin kasar Somaliya domin taimakawa a sake samar da zaman lafiya da wadata mai dorewa.

A wani bangaren kuma kwamitin sulhun MDD shi ma a ranar Laraban nan ya yi suka da babbar murya a kan wannan harin ta'addanci da aka kai da wata mota a kan tawagar ma'aikatan majalissar a Mogadishu, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, wadansu kuma suka jikkata sannan motocin suka lalace.

A cikin wata sanarwa da aka fitar, kwamitin tsaron majalissar ya jaddada kudurinsa na shawo kan duk wani nau'i na ta'addanci, tare da tabbatar da cewa, ta'addanci a ko wace siffa da salo yana cikin abubuwan da ke kawo barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya baki daya.

Kwamitin mai wakilai 15 ya nuna bukatar dake akwai na gurfanar da wadanda ke aikata wannan mummunar aikin, ko shiryawa ko ma ba da agajin kudin domin aiwatarwa, har ma da wadanda suke daukan nauyin masu aikata ta'addancin gaban shari'a, tare da kira ga sauran kasashe da yankuna da su ba da goyon bayansu sosai ta hanyar hada kai da juna wajen yakar ta'addanci. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China