in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Liberiya na son hada hannu da Sin game da samun sauki daga Ebola
2015-04-14 10:44:32 cri

Kasar Liberiya tana fatan yin hadin hannu da kasar Sin wajen bunkasa masana'antu masu zaman kansu, yadda kasar take kokarin samun sauki a kan Ebola da ta yi fama da ita, in ji shugaban kasar Ellen Johnson Sirleaf.

Madam Sirleaf ta fadi hakan ne lokacin da ta ziyarci cibiyar wasannin ta Samuel K. Doe, inda gwamnatin kasar Sin ta gina dakin shan magani domin yaki da cutar Ebola na kimanin kudin dala miliyan 41.

A cewar Madam Sirleaf, tattalin arzikin kasar ya dogara ne ga ci gaban masana'antu masu zaman kansu, don haka kasar ta Liberiya ke maraba da kasar Sin don kafa wadannan masana'antu.

Ta ce, kwanan nan gwamnatin kasar Sin ta ba da gudunmuwa na kayayyakin kusan dala miliyan 5 don taimakawa kasar farfadowa daga radadin Ebola, kuma a cewarta wannan gudunmuwa ba shakka ta fara shirya kasar na komawa cikin hayyacinsu, sannan za'a tattauna wannan kokari lokacin da za ta gana da shugabannin kasashen Guinea da Saliyo domin su tattauna dabarun da za su bullo da su bayan Ebola a kasar Amurka.

Shugaba Sirleaf ta ce, tsawon lokacin da kasar take fafutuka, kasar Sin tana tunawa da ita tare da taimaka mata. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China