in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda rikicin Iraki ke shafar fararen hula shi ne mafi muni a wannan karni, in ji UNICEF
2014-08-22 10:26:52 cri

Asusun kula da yara na MDD (UNICEF) ya ce, shaidun da fararen hulan da suka kaurace wa tashin hankalin da ke faruwa a lardin Sinjar da ke arewacin Iraki suka bayar, sun nuna yadda aka kashe jama'a, sacewa da kuma yiwa mata da yara fyade.

Kakakin MDD Stephane Dujarric, ya shaida wa taron manema labarai cewa, yadda ake gallaza wa mata da kananan kabilu a kasar ta Iraki a wadannan makonni, yana daya daga cikin munanan abubuwan da aka gani a cikin wannan karni.

Bugu da kari kakakin ya ce, hukumar ta adana wasu laifuffukan keta hakkin bil-adama 123 da kungiyar masu kaifin kishin Islama suka aikata kan Yazidawa da kungiyoyin kananan kabilu a Ninewa da ke kusa da kan iyaka da kasar Syria.

Kimanin 'yan Iraki miliyan 1.2 ne suka bar gidajensu a wannan shekara, ciki har da wasu mutane 600,000 da rikicin lardin Anbar da aka fara a watan Janairu ya kora da kuma wasu 600,000 da rikicin da ake fama da shi a ciki da wajen Mosul ya wargaza, da kuma rikicin Sinjar na baya-bayan.

A halin da ke ciki, hukumar samar da abinci ta MDD (WFP) da abokan huldar ta da ke yankin, sun kara yawan wuraren ciyar da jama'a a yankin Dahuk, inda ya zuwa yanzu hukumar ta samar da abinci ga mutane miliyan 2.5. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China