Wakilin ofishin asusun yara na MDD UNICEF a kasar Afirka ta Tsakiya CAR Souleymane Diabate, ya yi kira ga kasashen duniya da su tashi tsaye, wayen ganin an kawo karshen rikicin dake dada jefa yaran Afirka ta Tsakiya cikin mawuyacin hali.
Wakilin ofishin na UNICEF ya ce, akwai matukar bukatar gaggauta daukar matakan kare rayukan yaran Afirka ta Tsakiya, duba da halin rashin tabbas da rayuwarsu ke fuskanta sakamakon tashe-tashen hankula a kasar.
Mr. Diabate wanda ya bayyana hakan ga manema labaru a helkwatar MDD dake birnin New York, ya ce, yaran kasar na fuskantar matukar damuwa, bisa ga yadda suke ganin yadda ake yiwa al'umma kisan gilla tare da nuna tsantsar rashin tausayi.
Kididdigar da ofishin na UNICEF ya fitar dai ta nuna cewa, daga watan Disambar bara kawo wannan lokaci, an hallaka yara kanana a kalla 194, ciki hadda wadanda aka yiwa yankan rago. (Saminu)