in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin saman yakin Kenya ya kai hari kan sansanin Al-Shabaab dake kudancin Somaliya
2014-05-19 09:37:19 cri

A ranar Lahadin nan, jirgin saman yaki na kasar Kenya ya kai hari a sansanin kungiyar al-shabaab dake garin Jilib a kudancin kasar Somaliya, a ci gaba da ayyukan murkushe kungiyar da kwamitin samar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU take yi.

Wani mazaunin garin na Jilib wanda ya bukaci a sakaya sunan shi saboda tsaron lafiyar shi, ya ce, sun ga wucewar jiragen yakin na Kenya zuwa kauyen Maano-Gaabo, wanda nan ne sansanin kungiyar ta Al-Shabaab, mai alaka da Al-Qaida, inda daga nan kawai suka rika jin karar fashewar abubuwa, amma mutumin ya ce, bai san ko akwai wadanda suka jikkata ba.

Kauyen Maano-Gaabo yana da nisan kilomita 5 ne daga arewacin garin Jilib a kudancin yankin Somaliya a tsakiyar Juba, sannan tazaran kilomita 320 daga babban birnin kasar. Wannan gari na Jilib na daya daga cikin garuruwan da har yanzu suke karkashin tsaron soja.

Wata kungiya dake karkashin Al-Shabaab ta yanar gizo ta tabbatar da harin, amma ta ce, ba a samu sansaninsu ba, illa kawai ya fada akan gonakin ayaba, kuma babu wanda ya rasa ransa, bayanin da ba za'a iya tabbatar da shi ba. Su kuma mayakan Al-Shabaab din sun yi ikirarin cewa, sun kaucewa harin na jiragen Kenya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China