Rundunar 'yan sandan Najeriya ta gargadi masu nufin tada zaune tsaye da suka kauracewa hakan, ko kuma su hadu da fushin doka.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a jiya Laraba, gabanin zaben gwamnoni da 'yan majalissar jihohin kasar dake tafe a ranar Asabar mai zuwa.
Sanarwar ta kuma tabbatar da shirin rundunar, na cafke, tare da gurfanar da dukkanin wadanda aka kama da laifin karya dokokin zabe a gaban kuliya.
Rahotanni sun nuna cewa, a lokacin zaben shugaban kasar da ya gabata ranar 28 ga watan Maris, rundunar 'yan sandan kasar ta cafke mutane 67 a sassan jihar Kano, bisa zargin su da aikata laifuka da suka hada da satar katunan zabe, da kuma yawo da muggan makamai. Tuni kuma aka gurfanar da wadanda ake zargin gaban kotu domin su fuskanci shari'a. (Saminu)