Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, da ke ziyarar aiki a kasar Afrika ta Kudu, ya bayyana a ranar Laraba cewa, ya kamata Afrika ta samu wata yarjejeniyar adalci a MDD ta fuskar ikon fada a ji. Mista Mugabe ya fadin hakan ne a gaban manema labarai bayan wata ganawa tare da takwaransa na Afrika ta Kudu Jacob Zuma.
Afrika na ci gaba ga gabatar da shawara ta kawo sauye sauye a tsarin hawan kujerar na ki a kwamitin tsaro na MDD, in ji Mugabe, dake shugabancin kungiyar tarayyar Afrika (AU) da kungiyar ci gaban kudancin Afrika (SADC)
A yayin ganawar tasu, shugabannin biyu sun tattauna kan matsalolin shiyyoyi da na kasa da kasa da suke mai da hankali a kai a kai, musammun ma kan yanayin maido da zaman lafiya, da zaman karko, ta yadda za'a samu zarafin cimma burin dunkulewar shiyya, ci gaban masana'antu da ci gaban tattalin arziki da jin dadin zaman rayuwar shiyyar, da ma nahiyar Afrika baki daya.
A nasa bangare, mista Zuma ya bayyana cewa, shugabannin biyu sun tattauna kan batutuwan dake da janyo hankalin gamayyar kasa da kasa da shiyya shiyya, musammun ma kan bukatar kawo gyaran fuska a kwamitin tsaro na MDD a yayin da duniya ke shirin bikin cikon shekaru 70 na MDD a wannan shekara. (Maman Ada)