in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga kasashen Afirka da su karfafa shirin tsaron nukiliya
2015-03-25 09:39:34 cri

An bayyana samar da ka'idojin tabbatar da tsaron makamashin nukiliya a kasashen Afirka, a matsayin ginshikin dai zai taimaka wa kasashen nahiyar, amfana daga makamashin ta fuskar samar da lantarki, da sauran hidimomi da ba su shafi ayyukan soji ba.

Mwinjarubi Nyaruba, kwararre a fannin makamashin nukiliya daga Tanzaniya, shi ne ya gabatar da wannan kira, yana mai cewa, kiran ya zama dole ganin yadda a yanzu da dama daga kasashen Afirka, ke kokarin fara amfani da makamashin wajen gudanar da ayyukan fararen hula.

Nyaruba ya bayyana hakan ne yayin wani taron karawa juna sani da aka shirya a garin Arusha, dake arewacin kasar Tanzaniya. Ya ce, rashin samar da cikakkiyar kariya ga makamashin nukiliya na iya hana kasashen Afirka amfana daga fasahohin ci gaba masu alaka da nukiliya.

An dai shirya wannan taro ne bisa hadin gwiwar hukumar kula da harkokin nukiliyar kasar Tanzaniya TAEC, da kuma hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA.

An dai yi amfani da taron na wannan karo wajen tattaunawa game da manufofin tsaron nukiliya masu lakabin INSSPs. Kuma taron ya samu halartar masana da kwararru daga kasashen Afirka 27. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China