in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha ta dare matsayi na daya a yawan karbar 'yan gudun hijira
2014-08-20 10:35:50 cri

Hukuma mai kula da harkokin 'yan gudun hijira ta MDD, ta ayyana kasar Habasha a matsayin kasar da ta fi ko wace kasa a nahiyar Afirka yawan karbar 'yan gudun hijira.

A cewar kakakin babban jami'in MDD mai lura da harkokin 'yan gudun hijira Adrian Edwards, a halin da ake ciki, akwai 'yan gudun hijirar da yawan su ya kai 200,000 daga kasar Sudan ta Kudu, dake samun mafaka a Habasha tun cikin watan Disambar bara. Hakan kuwa a cewar Edwards kari ne kan 'yan Somaliya da na Eritrea, da su ma ke gudun hijira a kasar.

Jami'in ya kara da cewa, hukumar da hadin gwiwar mahukuntan kasar Habasha da sauran masu ruwa da tsaki, sun samar da sansanonin 'yan gudun hijira 23, da wasu karin wuraren wucin gadi 5 a sassan kasar daban daban.

A daya hannun kuwa Edwards ya ce, ambaliyar ruwa da ta aukawa wasu 'yan gudun hijirar su kimanin 10,000, ta haddasa matsaloli masu alaka da kiwon lafiya, matakin da ya sanya hukumar da hadin gwiwar daukacin masu ruwa da tsaki fara aikin janye ruwa zuwa wasu koramu da tafkuna, a kokarin kaucewa barkewar cututtuka masu yaduwa sakamakon karancin tsafta. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China