in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha ta dauki aniyar kawar da auren yara kanana
2014-07-23 10:26:01 cri

Mataimakin firayin ministan kasar Habasha Demeke Mekonne ya ce, nan da shekara ta 2025, kasarsa ta za ta kawar da auren yara kanana da kuma kaciyar mata.

Mataimakin firayin ministan ya bayyana wannan mataki da kasarsa za ta dauka a wani taron koli na duniya, wanda gwamnatin Britania da asusun kula da yara na MDD UNICEF suka shirya a birnin Landan.

Mekonnen ya ce, za su cimma burinsu ta hanyar aiki kafada da kafada da iyayensu, da kuma al'umma baki daya domin murkushe wadannan dabi'u gaba daya.

A yayin da take jawabi, ministar al'amurran mata da yara da matasa ta kasar Habasha, Zenebu Tadesse, ta ce, kididdiga ta nuna cewar, kaciyar mata ta ragu a tsakankanin yara 'yan matan da ba su kai shekaru 14 ba, daga kashi 52 bisa dari a shekarar 2000, ya zuwa kashi 23 bisa dari a shekarar 2011.

Ministar ta kuma kara da cewar, a bangaren auren wuri da ake yiwa 'yan mata shi ma ya yi kasa daga kashi 33.1 bisa dari a shekarar 1997, ya zuwa kashi 21.4 bisa dari a shekarar 2010.

Taron kolin na Landan ya samu halartar matasa da wakilan al'umma da masu kare hakkin bil'adama, da kuma shugabannin gargajiya da na addinai, har ma da shugabannin gwamnatoci da masu fada a ji na duniya, gami da kwararru da kuma masu jagorar kare hakkokin mata da yara. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China