Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya Farfesa Attahiru Jega, ya jaddada kudurin hukumarsa, na ci gaba da daukar karin matakan dakile duk wasu matsaloli da ka iya bullowa, yayin zaben gwamnoni, da na 'yan majalissun jihohin kasar da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.
Farfesa Jega, ya bayyana hakan ne yayin da mambobin kwamitoci 2, na majalissar dokokin tarayyar kasar, wadanda suka sanya ido a zaben da ya gabata suka kai masa ziyara a ofishinsa. Ya kuma kara da cewa, INEC za ta kokarta wajen warware matsalolin da ta fuskanta, yayin zaben shugaban kasa da ya gabata a ranar 28 ga watan Maris. (Saminu)