in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana zai jagoranci dandalin Sin da Afrika a Beijing
2014-07-31 10:09:45 cri

Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama zai jagoranci a cikin wannan shekara dandalin huldar dangantaka na kanana gwamnatocin larduna cikin gida na Sin da Afrika da za'a shirya a nan birnin Beijing daga ranar 27 zuwa 28 ga watan Agusta a wani labarin da kamfanin dillancin labarai na kasar Ghana ya rawaito a ranar Laraba.

Kungiyar jama'ar kasar Sin domin sada zumunta tare da kasashen waje za ta shirya wannan dandali cikin hadin gwiwa tare da kungiyar birane da gwamnatocin cikin gida na kasashen Afrika, kuma dandalin zai karfafa huldar dangantaka a bangaren cikin gida na Sin da Afrika.

Jakadiyar kasar Sin dake kasar Ghana, madam Sun Baohong ta yi wannan sanarwa a yayin wata ziyarar sada zumunci da ta kai wa Julius Debrah, ministan cigaban karkara na gwamnatin kasar Ghana a birnin Accra.

Musanya tsakanin kananan gwamnatocin cikin gida na Sin da Afrika ta taka muhimmiyar rawa wajen karfafa da raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika, in ji madam Sun, tare da kara bayyana cewa, wannan dandali zai kara daga abokantakar Sin da Afrika da dangantakar bangarorin biyu zuwa wani babban mataki.

Wannan dandali zai hada da wani taron shugabannin cikin gida na bangarorin biyu da dandalin tattalin arziki da kasuwanci da zai tattara mutane fiye da dubu daya, wadanda a cikinsu, akwai wakilan kungiyoyin da ba na gwamnatoci ba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China