in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hankula sun kwanta a fadin Najeriya bayan fargabar yanayin zabe
2015-04-07 09:12:33 cri

Rahotanni daga Najeriya na nuna cewa, yanzu haka hankula sun fara kwantawa, bayan da aka kammalar babban zaben kasar na karshen makon jiya lami lafiya.

A baya dai masu fashin baki da dama sun rika hasashen yiwuwar barkewar rikici yayin, ko bayan zaben, sai ga alama yanzu haka hankula na kara kwanciya, tun bayan bayyana sakamakon zaben na ranar 28 ga watan jiya.

A Abuja, fadar gwamnatin kasar, al'amura sun fara gudana kamar yadda aka saba, inda da dama daga kiristocin dake zaune a birnin suka gudanar da i'badu a bajami'un su a jiya Lahadi ba tare da wata matsala ba.

A cewar Kolawole Amao, daya daga wadanda suka halarci wata majami'i dake Abujan, mutane sun samu nutsuwa, wanda hakan ya ba su damar fita wajen ibada yadda ya kamata. Ya ce, 'yan Najeriya sun riga sun bude sabon shafi bayan kammalar zaben da ya zamo mai matukar tarihi a kasar.

Amao ya kara da cewa, sun yi farin ciki da al'amura suka daidaita, duba da cewa, da dama daga mutanen dake zaune a birnin sun koma gidajen su gabanin zaben, domin kaucewa abin da ka je ya zo.

Hukumomin kasa da kasa da suka sanya ido yayin gudanar babban zaben na Najeriya, ciki hadda MDD, da kungiyar AU da ECOWAS, sun jinjinawa tsarin sa, sun kuma shaida cewa, ya kammala cikin kwanciyar hankali. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China