Kasar Zimbabwe ta kori 'yan kasar Habasha 179 da suka shiga kasarta ba bisa doka ba a cikin watan Oktoban da ya gabata, in ji kafofin watsa labaran gwamnatin kasar.
'Yan kasar ta Habasha, 179 masu shekarun aifuwa tsakanin 15 zuwa 28, sun amince da cewa, sun taka dokokin kasar da suka shafi hijira kuma sun amince da laifin gaban alkali Tendai Mahwe a wannan makon, in ji jaridar The Herald.
Alkalin ya yi wa gungun kashedi kafin sanya su hannun hukumar da ke kula da bakin haure da za ta kula da mai da su kasarsu cikin gaggawa.
'Yan kasar Habasha, da suka nemi matsayin 'yan gudun hijira, sun bayyana cewa, sun gudu daga kasarsu dalilin tashe tashen hankalin siyasa.
Amma kuma alkalin ya ba su shawarar da su nemi takardun da suka dace kafin su shigo kasar Zimbabwe. (Maman Ada)