in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zambiya ya taya zababben shugaban Nigeriya murna
2015-04-03 09:58:20 cri

Shugaban kasar Zambiya Edgar Lungu ya taya zababben shugaban kasar Nigeriya Muhammadu Buhari da kuma shugaba mai barin gado Goodluck Jonathan a kan yadda suka mutunta bukatun al'ummarsu.

A cikin sakon taya murnan ga shugabannin biyu, Mr. Lungu ya ce, Zambiya tana goyon bayan tsarin demokradiyyar Nigeriya, da kuma bukatar zaman lafiya mai dorewa a kasar da ta fi yawan al'umma da kuma karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika baki daya.

Shugaban kasar ta Zambiya ya kuma yi kira a kan sabbin shugabannin na Nigeriya da su yi aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki domin hada kan kasa da tabbatar da an mika mulki lami lafiya.

Zambiya, in ji shi, a shirye take ta taimaki Nigeriya a dangantakar tsakanin su biyu, da ma sauran kasashe baki daya don tabbatar da mika mulkin cikin kwanciyar hankali da lumana, yana kuma mai yaba wa shugaban Goodluck Jonathan mai barin gado a kan yadda ya amince da zabin al'ummar kasar, yana mai cewa, hakan zai kara inganta demokradiya a kasar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China