in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cibiyoyin binciken kudi 20 na tantance lalitar kamfanin NNPC a Najeriya
2014-02-28 10:45:08 cri

Yanzu haka kimanin cibiyoyin binciken kudi 20 ne, ke gudanar da aikin tantance asusun kamfanin sarrafa man fetir na tarayyar Najeriya NNPC. Hakan dai ya biyo bayan umarnin da majalissar dattawan kasar ta bayar, na daukar matakan gano gaskiyar zargin bacewar dala miliyan dubu 20 daga lalitar kamfanin.

Babban mai binciken kudin kasar Samuel Ukura ne ya tabbatar da hakan, yayin da ya bayyana gaban kwamitin lura da asusun kasa na majalissar wakilan kasar a jiya Alhamis, domin kare kasafin kudin kasar na shekarun 2013 da 2014.

A makon da ya gabata ne dai shugaban tarayyar Najeriyar Goodluck Jonathan, ya dakatar da gwamnan babban bankin kasar Lamido Sanusi daga mukaminsa, bisa zargin karya dokokin aikin.

Kafin hakan kuwa gwamnan babban bankin na CBN ya zargi kamfanin na NNPC da kin sanya wadancan kudade ne, da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan dubu 20 cikin lalitar gwamnatin tarayya. Matakin da ya janyo sa in sa tsakanin sa da fadar gwamnati.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Sanusi Lamido ya zargi NNPC da aikata badakala ba, wanda hakan ya kai ga shugaba Jonathan umartar sa da ajiye aiki cikin watan Disambar bara, kafin daga bisani ya dakatar da shi cikin makon da ya gabata. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China