in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin da aka kai a Kenya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 147
2015-04-03 09:45:41 cri

Ministan harkokin cikin gida na kasar Kenya Joseph Nkaissery ya furta cewa, harin da aka kai a ranar Alhamis din nan, kungiya Al-shabab ce ta Somaliya ta kai shi a kan jami'ar Moi da ke birnin Garissa a yankin arewa maso gabashin kasar, abin da ya haddasa mutuwar mutane da dama

Mr Nkaisseryyace, a sanyin safiyar wannanrana misali karfe 5 da rabi na asuba, 'yan bindiga 4 masu dauke da bom sun kutsa cikin jami'ar Moi, inda suka kai harin ga dalibai da ba sa bin akidarsu. Daga bisani kuma sojojin Kenya suka yi musu kofar rago a jami'ar, inda aka shafe awoyi 16 ana kokarin dakile 'yan ta'adda tare da ceton jama'a. Harin da aka kai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 147, tare da jikkatar wasu 179, an riga an kai masu jikkata zuwa asibitin da ke birnin Nairobi don yin musu jinya. Sojojin sun kuma ceci mutane sama da 500,aka kuma harbe 'yan bindigar 4 har lahira.

A wannan rana, kungiyar Al Shabab ta sanar da daukar alhakin batun, inda ta ce dauki wannan mataki ne don ramuwar gayya ga farmakin da gwamnatin Kenya ta kai ga kungiyar.

Dangane da wannan harin, magatakardar MDD Ban Ki-Moon yaba da wata sanarwa ta kakakinsa, inda ya yi Allah-wadai da wannan hari, tare da bukaci a gurfanar da masu laifi gaban kuliya.

A cikin sanarwar, Ban Ki-Moon ya sake nanata goyon bayansa ga gwamnatin Kenya da jama'arta, kuma ya bayyana cewa, M.D.D. za ta ci gaba da taimakawa kasar da sauran kasashen da ke yankin don yaki da ta'addanci da 'yan tsageru, da kuma masu tsattsauran ra'ayin addini.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China