in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi kira a tabbatar da zaman lafiya bayan samun sakamakon zaben Nigeriya
2015-04-02 10:16:38 cri

Shugaban kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU Madam Nkosazana Dlamini Zuma ta yi kira ga dukkanin shugabanni da jama'a da su tabbatar da zaman lafiya bayan samun sakamakon babban zaben da aka gudanar a Nigeriya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Madam Zuma ta ce, ta bi tsarin zaben sau da kafa, ta idon wakilan kungiyar da suka je aikin sa ido a kai da Farfesa Amos Sawyer da Farfesa Ibrahima Fall suka yi aiki tare da sauran shugabannin Afrika wanda ya kai ga jefa kuri'an a ranakun 28 zuwa 29 ga watan Mayu.

Shugaban kwamitin ta yaba wa 'yan Nigeriya bisa ga hakurinsu da kuma kokarin da suka yi na aiwatar da zaben cikin lumana, sannan kuma suka tabbatar da dan hatsaniyar da aka yi bai dakushe aniyarsu wajen zaben ba a kasar. Madam Nkosozana Dlamini Zuma ta kuma jinjina wa hukumar zaben mai zaman kanta ta kasar Nigeriya INEC saboda wannan gaggarumar nasara da ta samu ta aiwatar da zaben lami lafiya, duk da kalubalolin da suka fuskanta. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China