in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Faransa ya taya murna ga zababben shugaban Najeriya
2015-04-02 10:51:17 cri

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya yi hira ta wayar tarho a ranar Laraba tare da Muhammadu Buhari, wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta sanar da cewa, shi ne ya lashe zabe, a cewar wata sanarwa ta fadar Elysee a ranar Laraba.

Shugaban Faransa ya taya Muhammadu Buhari murna kan nasarar da ya samu, tare da bayyana jin dadinsa kan yadda zabe ya gudana, lamarin da ya nuna cewa, demokaradiyya ta samu gindin zama a Najeriya.

Shugaban Faransa ya tabbatar wa sabon shugaban Najeriya niyyar Faransa ta ci gaba da huldar dangantakar tare da shi kamar yadda ta kasance tare da shugaban kasar mai barin gado Goodluck Jonathan. Haka kuma ya jaddada cewa, Faransa za ta ci gaba da tallafa wa Najeriya, da ma kasashe makwabtanta kan kokarin da suke na yaki da kungiyar Boko Haram, in ji sanarwar fadar Elysee. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China