Afrika ta Kudu ta jaddada goyon bayanta a game da kokarin da kasashen duniya ke yi na yaki da ta'addanci.
Gwamnatin ta Afrika ta Kudu ta bayyana wadannan kalaman ne a sakamakon farmakin ta'addanci da aka kai a kasashen Pakistan da Australia.
Gwamnatin Afrika ta Kudu ta yi allah wadai da hare-haren da aka kai da kakkausar murya, kamar dai yadda kakakin ma'aikatar harkokin waje da ci gaba ta Afrika ta Kudu Clayson Monyela ta bayyana.
Monyela ta ce, Afrika ta Kudu ko kadan ba za ta lamunta da sifofin ta'addanci daga ko wane bangare. (Suwaiba)