Kasar Najeriya ta rufe kan iyakokinta na kasa da na ruwa tun daga ranar 26 har zuwa 28 ga watan Maris dalilin zabukan da za su gudana, in ji hukumar kula da harkokin shige da fice ta kasar Najeriya (NIS) a ranar Laraba.
David Parradang, babban mai sa ido a hukumar NIS, ya kuma bukaci 'yan kasashen waje dake zaune a Najeriya, musammun ma wadanda suka fito daga kasashe makwabta kamar su Kamaru, Nijar da Chadi da su kiyaye shiga harkokin zabuka.
Zaben shugaban kasar Najeriya zai gudana a ranar 28 ga watan Maris, kafin zaben gwamnoni da na 'yan majalisu da aka tsaida shiryawa a ranar 11 ga watan Afrilu. (Maman Ada)