Gwamnatin kasar Cote d'Ivoire ta bukaci a ranar Talata 'yancin shiga har cikin kasar Liberiya domin tabbatar da tsaron yankin dake kudu maso yammacin kasarta dake fama da hare haren mutane masu dauke da makamai a kan iyakar kasashen biyu.
Idan muka samu wannan 'yancin shiga, ta hanyar sintirin hadin gwiwa, sojojinmu za su samun 'yancin shiga har wajen iyakar domin farautar masu tada kayar baya dake zuwa su gurbata kwanciyar hankalinmu, in ji ministan cikin gidan Cote d'ivoire Hamed Bakayoko a yayin wani zaman taron bangarori hudu tsakanin hukumomin Cote d'Ivoire, Liberiya da jami'an tawagogin MDD dake kasashen biyu.
Bisa kalaman ministan, kwamitin tsaron kasa ya dauki matakan da suka dace, kuma an ba da kayayyakin aikin ga jami'an tsaron Cote d'Ivoire domin share fadin yankin kan iyaka da kasar Liberiya.
A yayin wani rangadin aiki a ranar Jumma'a a yankin kudu maso yammacin kasar, shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya tabo shi da kansa batun, tare da bayyana fatan ganin kasarsa ta samu 'yancin farautar masu tada kayar baya har cikin kasar Liberiya.
Mista Ouattara ya kwatanta matsalar da ake ciki a halin yanzu da irin matsalar Nijar da Chadi da suka samu 'yancin shiga Najeriya, a cikin yakin da suke da mayakan kungiyar Boko Haram. (Maman Ada)