Shugaban hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta a Najeriya farfesa Attahiru Jega, ya ce, hukumarsa ta shirya caf, don gudanar da zaben da zai zamo mafi tsafta da karbuwa a tarihin kasar.
Jagoran hukumar ta INEC wanda ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki a jiya Laraba, ya ce, dage zaben kasar da aka yi a baya, ya ba su damar tanadar karin tsare-tsare na musamman, wanda za su taimakawa nasarar zaben.
Ya ce, cikin sabbin dabarun da INEC ta bullo da su, akwai inganta aikin ba da katunan kada kuri'u na din din din, aikin da a cewar sa yanzu haka ya kai kusan kaso 82 bisa dari. Kaza lika hukumar ta yi gwajin na'urar tantance masu kada kuri'u a sassan kasar daban daban, tare da horas da karin ma'aikatan wucin gadi yadda za a yi amfani da na'urar.
Sauran fannonin da INEC din ta inganta sun hada da ilmantar da masu kada kuri'u yadda zaben zai gudana, da kuma tsara yadda za a sada dukkanin mazabun kasar da kayan aiki.
Shugaban na INEC ya kuma bayyana cewa, za su samar da bayanan yadda zaben kasar ke kasancewa ta yanar gizo ga masu sha'awar sanin halin da ake ciki tun daga mataki na mazabu, a hannu guda kuma an kaddamar da wata manhajar wayar salula mai lakabin "MyINEC App" wadda masu wayar salula za su iya saukewa kan wayoyinsu, su kuma rika samun bayanan zaben kai tsaye.
Farfesa Attahiru Jega ya yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki, da su ba da gudammawarsu, wajen cimma gudanar sahihin zabe mai cike da adalci kuma cikin kyakkyawan yanayi. (Saminu)