Kungiyar tarayyar Turai EU, kasashen Swtzerland da Amurka ta bakin ofishin jakadancinsu dake Burundi sun soki tashin hankalin da ya faru kwanan nan a garin Cibitoke dake arewa maso yammacin kasar, da kuma Ruyigi dake gabashin kasar.
A cikin sanarwar hadin gwiwwa da ofisoshin suka fitar, kungiyar ta EU da kasashen Amurka da Switzerland sun nuna takaicinsu game da yawan wadanda wannan rikicin ya rutsa da su, tare da yin suka da babbar murya a kan ko wane irin tashin hankali da ka iya kunno kai a nan gaba.
A farkon wannan watan ne dai fada ya kaure na kwanaki 4 a Cibitoke dake tsakanin jamhuriyar demokradiya ta Kongo da Burundin, abin da ya kawo asarar rayuka mutane 99 da suka hada da wasu masu dauke da makamai su 95, sojoji 2, sannan fararen hula 2.
Har ya zuwa yanzu dai ba a san sunan jagorar kungiyar masu makaman ba, balle ita kanta kungiyar. A ranar 4 ga wannan watan ne dai a yankin Ruyigi dake gabashin wannan kasa ta Burundi, aka kashe wasu mayakan sa kai na jam'iyyar dake mulki uku, lokacin da 'yan bindigogi biyar suka afka wa wata mashaya.
Wadanda ke mashayar sun kama su, suka daure kafin su harbe su da cinna wa tutar jam'iyyar, da ma ofishin ta wuta a Ndemeka dake yankin Gisuru.
A cikin sanarwa, su kungiyar tarayyar Turai, Amurka da Switzerland sun bukaci 'yan siyasan Burundi da su tattauna a tsakanin su domin tabbatar da yarjejeniyar Arusha, da kuma fitar da tsarin zabe a nan gaba. (Fatimah)