Rundunar 'yan sanda a tarayyar Najeriya, ta ce, jami'anta za su tabbatar da takaita zirga-zirgar ababen hawa a ranekun manyan zabukan kasar dake tafe.
Dokar, a cewar kakakin rundunar Emmanuel Ojukwu, za ta fara aiki ne tun daga karfe 8 na safe ya zuwa karfe 5 na yammacin ranekun zaben. Zabukan da suka hada da na shugaban kasa, da 'yan majalissar tarayya dake tafe a ranar Asabar mai zuwa. Yayin da kuma za a kada kuri'u a zaben gwamnoni, da na 'yan majalissar dokokin jihohin kasar a ranar 11 ga watan Afirilu.
Ojukwu ya ce, dokar takaita zirga-zirgar za ta shafi daukacin al'ummar kasar, in banda motocin safarar marasa lafiya, da na kashe gobara, da kuma wasu ababen hawa da ake amfani da su wajen gudanar da ayyuka na musamman.
Rundunar ta bukaci masu anfani da hanyoyin mota, da su lura da wannan sanarwa gabanin zuwan ranekun zaben. Rundunar ta kuma ce, tana ci gaba da daukar dukkanin matakan da suka wajaba, domin tabbatar da cikakken tsaro a lokutan zabukan kasar. (Saminu)