in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nigeriya ba za ta rufe sararin samaniyarta ga jirgin sama ba lokacin zabe
2015-03-19 10:22:18 cri

Gwamnatin Nigeriya ta ce, a lokacin babban zaben dake tafe, ba za ta rufe sararin samaniyarta ga jiragen sama ba, kamar yadda ministan cikin gida Abba Moro ya tabbatar wa jami'an diplomasiyya lokacin wata ganawa tsakanin su a Abuja, babban birnin kasar.

Abba Moro ya ce, gwamnatin kasar za ta yi hakan ne kadai idan akwai bukata saboda karfafa matakan tsaro, yana mai tabbatar da cewar, kasar za ta tabbatar da an ba da tsaron da ya kamata a kan iyakokinta kafin da kuma bayan zabe, musamman saboda rahotannin sirri dake cewa, wassu 'yan kasashen waje na dauke da katunan zabe na din din din da hukumar zaben kasar ta bayar

Minista Moro a don haka ya yi kira ga kasashen Chadi, Kamaru, Jamhuriyar Benin da Nijar da su ba da kariya kan iyakokinsu daga nasu bangaren, yana mai jaddada cewa, zirga-zirga a lokacin zaben za'a tattauna a kan haka tsakanin hukumomin da hakan ya shafa. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China