Rahotanni daga Nigeriya sun tabbatar da cewar, a kalla mutane 10 sun hallaka lokacin wani harin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a garin Gamboru na jihar Borno dake kan iyaka da kasar Kamaru kamar yadda majiyar tsaro ta tabbatar.
Harin da aka kai kasa da makonni uku bayan da sojojin kasar Chadi dake aikin hadin gwiwwa suka tarwatsa maboyar 'yan kungiyar, in ji wannan majiya, sai da wassu sojojin Kamaru suka kai dauki, duk da hakan mutane 10 sun riga sun hallaka.
A Laraban wannan makon ne dai wannan harin ya afku bayan da sojojin Nigeriya suke ta samun nasarar kore 'yan kungiyar daga kusan dukkan garuruwan da suka kame a baya a wani kokarin da ake na kakkabe su kafin babban zaben kasar dake tafe a mako mai zuwa.
Shugaban Nigeriya Goodluck Jonathan wanda yake son ya sake dawowa karagar mulki ya je zawarcin zaben jama'ar garin Damaturun jihar Yobe a ranar Alhamis din nan tare da musu alkawarin kawo karshen wannan rashin hankalin 'yan Boko Haram da suka yi ta fama da shi. (Fatimah)