Rahotanni daga garin Bama na jihar Bornon taraiyyar Nigeriya sun tabbatar da cewa, 'yan kungiyar Boko Haram sun hallaka matan da suka aura dole a wannan gari ganin yadda sojoji ke kara matsowa daf da maboyarsu bayan sun kwace garin daga hannun 'yan kungiyar.
Kamar yadda wani ganau ya tabbatar a ranar Alhamis din nan ya shaida wa Xinhua cewa, mayakan sun ce sun aikata wannan danyen aikin ne a kan matan da suka sato ta hanyar hare hare da yin garkuwa da su lokacin samamen da suka yi ta yi a garin, domin kada su auri wadanda ba su yi imani ba.
Kafin dai su hallaka matan, sai da 'yan kungiyar suka gaya masu cewa, ba za su bar ko dayan su a raye ba saboda idan wadanda ba su yi imani suka aure su, idan suka je aljanna, ba za su iya zama tare da su ba, in ji wannan majiya.
Sojojin Nigeriyan sun afka garin na Bama jim kadan bayan aikata wannan danyen aikin na kungiyar, sai dai an samu nasarar karbe garin daga wajen su, kuma har yanzu ana kan tabbatar da an kakkabe su gaba daya daga wannan yankin, in ji wani jami'in tsaro a bayanin da ya yi wa Xinhua a Maiduguri, hedkwatar Bornin..
Bayan wannan samame, jami'an tsaro sun kwato makamai da dama daga maboyar 'yan kungiyar. (Fatimah)