Kwararrun kasashe tara na nahiyar Afrika suka yi taro a ranar Alhamis a Libreville, babban birnin Gabon, bisa tsarin da ya shafi taron shirin "Roll Back Malaria" (RBM) karo na goma sha daya, dake da manufar kara tattara kudade domin yaki da zazzabin cizon sauro. Haduwar ta kunshi kwararru daga kasashen Kamaru, Congo, Afrika ta Tsakiya, RDC, Gabon, Sao Tome, Chadi, Guinee-Equatoriale da Burundi.
Duk da cewa Malaria cuta ce dake barna a wadannan kasashe, samun kudaden yakar cutar na ja da baya, dalilin bullo da tunanin tattara kudade a cikin gida domin yaki da wannan babban abokin gaba, in ji shugaban shiyyar tsarin RBM da ake kira kuma CARN, dokta Jose Nkuni Zinga.
A cewarsa, cimma burin MDGs, da ya shafi rage cutar zazzabin cizon sauro da kashi 75 cikin 100, ko da yake abu ne maras tabbas. Haka kuma ta wani bangare, jami'in ya nuna cewa, Gabon da Congo ba za su kasance ba cikin kasashen da za su samu kudaden asusun yaki da cutar Malaria da ciwon tari na kasa da kasa ba, a cewarsa, hakan watakila na da nasaba da yadda kasashen biyu suka yi amfani da kudaden asusun na baya bayan nan. (Maman Ada)