Masana masu binciken cututuka sun fitar da sakamakon wani bincike da ya girgiza duniya, sakamakon ya gano cewar, kafa kariyar yaki da kwayoyin cutar zazzabin malaria a jikin bil'adama ya dogara ne a kan bangaren duniyar da mutum yake da zama.
Shugaban binciken cututtuka na cibiyar bincike ta zauren Walter da Eliza dake Melbourne a Australia, Dr. Ivo Mueller, wanda mamba ne na tawagar masanan da suka gudanar da binciken na duniya ya ce, binciken wanda ya dauki shekaru 10 yana yi a kasashe 11, ya binciki rayuwar kusan mutane dubu 12, inda masanan suka duba kwayoyin halittun jama'a, domin gano kwayoyin dake sanya jikin bil'adama kafa kariya cutar a jikinsa.
Dr. Mueller ya kara da cewar, Afrika ita ta zamanto wurin da zazzabin Maleriya ya fi kamari a duk duniya, kuma sauran kasashen da wannan cutar ke banna sun hada da wasu sassa na Papua New Guinea da kasar Indonesia.
Mueller ya ce, sakamakon bincike ya nuna cewar, jama'ar Afrika ba ta da kwayoyin halittar da ake da su a wasu kasashe, wadanda ke kafa kariyar cutar malariya a jikin bil'adama.
Cutar zazzabin Malariya wacce ke samu nasarar murkushe bazuwarta a wasu sassa na duniya, har yanzu tana ci gaba da kashe mutane dubu 300 zuwa dubu 500 a kowace shekara. (Suwaiba)