in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun kwato garin Bama daga mayakan Boko Haram
2015-03-17 09:46:35 cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojojin kasar sun kwato garin Bama dake jihar Borno daga hannun mayakan kungiyar nan ta Boko Haram.

Cikin wani sakon tiwita da kakakin ma'aikatar tsaron kasar Manjo Janar Chris Olukolade ya fitar, an ce, sojojin sun fatattaki mayakan Boko Haram daga garin na Bama ne a jiya Litinin. Ya ce, dakarun hadin gwiwa na kasar Chadi sun nausa kan iyakar kasar, domin farautar mayakan kungiyar da suka tsere.

Kaza lika Olukolade ya bayyana cewa, sojojin na ci gaba da bincike, da kaddamar da hare-hare a maboyar 'ya'yan kungiyar ta kasa da sama.

Garin na Bama dake jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya dai shi ne birni na biyu mafi girma a jihar.

Rahotannin baya bayan nan na nuna cewa, dakarun Najeriyar na samun nasarori a yakin da suke yi da 'yan Boko Haram, a sassan jihohin Borno, da Yobe da kuma Adamawa. Inda baya ga kwace yankuna, sojojin na kuma amshe, tare da gano tarin makamai da mayakan ke amfani da su. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China