Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya sanar a ranar Laraba da nadin wasu sabbin ministoci takwas bisa wani yunkurin kawo gyaren fuska ga gwamnatin wannan babbar kasa da ke yammacin nahiyar Afrika.
Shugaban kasar dai ya dora wa wadannan sabbin ministocin takwas nauyin rike madafun iko, jim kadan kafin fara taron ministoci na mako mako a birnin Abuja, hedkwatar mulkin kasar.
Daga cikin sabbin ministocin da aka nada, akwai Musiliu Obanikoro, daya daga cikin ministoci bakwai da suka yi marabus daga gwamnati a shekarar da ta gabata domin takarar zama gwamna.
Mista Obanikoro, da ba a zabe shi ba gwamna a cikin jiharsa ta Lagos na rike da mukamin ministan harkokin wajen kasar a halin yanzu.
A lokacin baya dai ya rike kujerar ministan tsaron kasa, kana ya taba zama jakadan kasar Najeriya da ke kasar Ghana.
Zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisan kasar Najeriya za su gudana a ranar 28 ga watan Maris, a yayin da zabukan gwamnoni da na 'yan majalisun jahohi za su gudana a ranar 11 ga watan Afrilu. (Maman Ada)