Rahotanni na nuna cewa, sojojin Nigeriya a yankin arewa maso gabashin kasar suna ta samun nasarar karar fatattakar 'yan kungiyar Boko Haram daga yankin, kamar yadda majiyar tsaro ta tabbatar a ranar Lahadi.
Kakakin tsaron kasar Manjo Janar Chris Olukolade a wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi ya ce, sojojin sama suna ci gaba da yin luguden wuta a maboyar kungiyar da aka gano a jihohin Yobe da Borno a wani mataki na yaki da 'yan ta'addar.
Janar Olukolade ya ce, ana kara bin sawun inda sojojin saman suka yi luguden wuta don a tabbatar an kakkabe wadannan 'yan ta'adda, mamaye na baya bayan nan na zuwa ne sakamakon yarjejeniyar da aka cimma ta hadin gwiwwa tsakanin shugabannin Nigeriya, Chadi, Kamaru da jamhuriyar Niger, wato za a dauka matakin bai daya don mai da martani a kan kungiyar da ya zuwa yanzu ta hallaka mutane sama da 13,000, tare da kore da dama daga muhallansu.
Kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU a zaman da ta yi a watan Janairu ya zartas da shawarar kafa sojojin hadin gwiwwa kashi na farko 7,500 domin yakar kungiyar ta Boko Haram. (Fatimah)