Sojojin Nigeriya da hadin gwiwwar sojojin kasashen dake makwabtaka da ita suna yin artabu da 'yan kungiyar Boko Haram masu dauke da makamai a kokarin kwato garin Damasak a ranar Lahadin nan, kamar yadda majiyar tsaro mai tushe ta tabbatar wa kamfanin dillancin labari na Xinhua cewa, an yi gaggarumin bata kashi tsakanin jami'an tsaron hadin gwiwwa da mayakan.
Damasak dai garin dake aikin noma yana kan iyaka ne da jamhuriyar Niger, kuma 'yan kungiyar ta Boko Haram suka kwace shi a shekarar bara lokacin da suka kai farmaki a garuruwan kan iyaka dake jihar Borno, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 50.
Kakakin sojin a Nigeriya ya tabbatar da cewar, har yanzu ana kan arangama wadda aka fara a ranar Lahadin da ta karyata rahotannin makon jiya da ke cewa, sojojin hadin gwiwwar sun riga sun kwato garin. (Fatimah)