in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarorin da ke gaba da juna a Libya na tattaunawa a Algiers
2015-03-12 09:39:54 cri

A jiya ne bangarorin siyasar kasar Libya suka fara wata tattaunawa a birnin Algiers na kasar Algeria da nufin warware takaddamar da ke tsakaninsu.

A jawabinsa yayin taron manema labarai, ministan kasar Algeria mai kula da yankin Maghreb da harkokin da suka shafi kasashen Afirka Abdelkader Messahel ya bayyana cewa, mahalarta taron sun bayyana kudurinsu na kare hadin kan kasar, yaki da duk wasu ayyukan ta'addanci da kokarin ganin an kafa gwamnatin hadin kan kasa ba tare da bata lokaci ba.

Messahel ya ce, wannan wata alama da ke nuna cewa, kasar ta Libya tana bukatar zaman lafiya, kuma za ta warware matsalolinta ba tare da tsoma baki daga wata kasa ta ketare ba.

A jawabinsa, manzon musamman na MDD da ke Libya Bernardino Leon ya yaba taron na birnin Algiers, ganin yadda kowa ya yi imanin cewa, hawa teburin tattaunawa ita ce hanya guda ta magance matsalar kasar, maimakon daukar matakan soja.

Bugu da kari mahalarta taron sun bayyana damuwa game da tabarbarewar yanayin tsaro a Libya, da kuma yadda ake samun karuwar ayyukan ta'addanci.

Yayin taron na yini biyu wadda MDD ta shirya, shugabannin siyasu 20 da masu kare hakkin bil-adama sun amince da yarjejeniyar Algiers wadda ta nanata bukatar mutunta shirin siyasar kasar kamar yadda tsarin demokiradiya ya tanada, da kuma mika mulki ga hannun farar hula cikin lumana. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China