in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a ci gaba da tattaunawa tsakanin masu gaba da junan Libya a Morocco
2015-03-09 10:49:28 cri

Bangarori masu gaba da juna na kasar Libiya za su sake komawa kan tebur a ranar Laraba mai zuwa a kasar Morocco, shawarwarin siyasar sun rataya kan cimma wata mafita game da rikicin siyasar Libiya. Wata sanarwar tawagar ba da tallafi ga Libiya ta MDD (UNSMIL) ta jaddada a ranar Lahadi cewa, kwanaki uku na tattaunawar siyasa, da aka kammala a ranar Asabar a birnin Skhirate na kasar Morocco, sun kasance masu alfanu da darasi.

Sanarwar ta cigaba da cewa, bangarorin da suka taru a karon farko a cikin zaure guda, za su sake komawa kan teburin shawarwari a ranar Laraba mai zuwa a kasar ta Morocco, bayan an huta a ranakun Litinin da Talata. Wannan hutu zai taimakawa bangarorin Libiya kimanta ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu, da kuma tattaunawa tare da tawagoginsu kan yadda za'a kai kasar bisa tudun mun tsira cikin wadannan shawarwari, in ji tawagar UNSMIL, da ta bayyana cewa, shawarwarin sun mai da hankali kan hanyoyin daidaita matsalar tsaro domin kawo karshen yake yake da kafa wata gwamnatin hadaka domin kawo karshen rarrabuwar hukumomin wannan kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China