in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya sanar da garambawul a gwamnatinsa
2014-10-23 11:05:38 cri

Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya sanar a ranar Laraba da wani karamin garambawul na mambobin fadarsa, musammun ma domin maye gurbin ministocin da suka yi murabus yau da mako guda da ya wuce.

Shugaban Najeriya ya sanar da wadannan nade-nade a ranar Laraba a yayin zaman taron mako mako na kwamitin zartarwa na tarayya (FEC). Sakatariyar kasa kan harkokin waje, Viola Onwuliri, za ta maye gurbin Neysom Wike a mukamin ministan ilimi. Tsohon ministan kasa ya bar mukaminsa domin mai da hankali kan fagen siyasa a jiharsa. Nurdeen Mohammed, sakataren kasa kan harkokin waje, zai rike kujerar ministan watsa labaru har zuwa lokacin nada sabon ministan.

Wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana cewa, shugaban Najeriya ya kuma bukaci ministan harkokin musamman, Taminu Turaki da ya kula da kujerar ministan kwadago, a yayin da ministan kasuwanci da masana'antu da zuba jari, Olusegun Aganga, zai hada mukaminsa da mukamin ministan kasa kan masana'antu, kasuwanci da zuba jari da mista Samuel Ortom ya bari.

Ministan tsaro, Aliyu Guasu, zai hada kujerarsa tare da ta ministan kasa kan tsaro, bayan murabus din mista Musiliu Obanikoro. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China