Helkwatar tsaron Najeriya ta ce, dakarun sojin kasar na daf da karasa murkushe kungiyar Boko Haram, biyowa bayan nasarorin da take samu a baya bayan nan a kan mayakan kungiyar.
Kakakin rundunar tsaron kasar Manjo Janar Chris Olukolade ne ya shaidawa manema labarai hakan, yayin wani taron 'yan jaridu da ya gudana a birnin Abuja, fadar gwamnatin kasar.
Olukolade ya ce, ba ja da baya game da kwazon da sojojin Najeriyar ke yi a wannan yaki, kuma ba da wani jinkiri ba za a kakkabe ragowar mayakan Boko Haram daga Najeriya, da ma sauran makwaftanta dake fuskantar barazanar kungiyar.
Daga nan sai ya ja hankalin 'yan jaridu da su kauracewa masu kushe himmar da dakarun Najeriya ke nuna wa, mutanen da ya ce ba sa fatan ganin an cimma nasarar wannan yaki.
Ya ce, Najeriya ce ta shirya ayyukan sojin dake gudana, kafin sauran kasashe su shiga aikin domin ba da tasu gudumma, karkashin shirin hadin gwiwa na MNJTF.
Cikin matakan da rundunar sojin Najeriyar ke dauka a baya bayan nan dai hadda kaddamar da hare-hare ta sama, tare da kai simame ta kasa a sansanoni da maboyar mayakan kungiyar ta Boko Haram, matakin da kakakin rundunar sojin ya ce ya haifar da babbar nasarar da ake fata. (Saminu)